Kai tsaye: Ivory Coast da Colombia

Wannan shafi na kawo muku sharhi kai tsaye kan wasan Ivory Coast da Colombia a rukunin C na gasar cin kofin duniya. Latsa nan domin samun sabbin bayanai.

Da wannan muka kawo karshen sharhin da muke kawo muku, sai a kasance da bbchausa.com a kodayaushe domin samun labaran gasar da ma sauran labarai.

Colombia 2-1 Ivory Coast

Tsohon dan wasan Faransa Thierry Henry ya ce "Ina ganin mun ga kasashe biyun da za su jagoranci rukunin C."

Jibril Abdullahi a shafinmu na BBC Hausa Facebook babu inda ksashen Afrika za su je

Har yanzu Colombia na ruwa domin rukunin na da hadarin gaske - kowacce kasa za ta iya kai labari, amma sai mun jira mun ga yadda wasan Japan da Greece zai kasance.

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

An tashi wasa Colombia 2-1 Ivory Coast. Wasa ya kai wasa, yayi dadin kallo, duka bangarorin sun taka rawar gani.

Dakikai kadan ne suka rage

Mintuna 90: Ana ta kai kora

Minuta 88: Ivory Coast sun samu bugun tazara amma Yaya Toure bai iya kaita ba

Aliyu Tanko a BBC Hausa rediyo: Akwai alamun fahimtar juna tsakanin 'yan wasan Ivory Coast - ganin yadda Drogba ya barwa Toure kanbun kyaftin sabanin yadda ta faru da Yobo na Nigeria da Enyeama.

85: Ivory Coast sun kara kai kora amma babu labari

Mintuna 83: Colombia 2-1 Ivory Coast - Kora bayan kora Ivory Coast suke ta kaiwa.

Saura minti goma a tashi - Colombia 2-1 Ivory Coast - ko Colombia za su kai labari

Mintuna 78: Mun ga an zira kwallaye masu kyau a wannan gasar amma babu shakka kwallon Gervinho na sama-sama. Ko Didier Drogba ada Salomon Kalou za su sa a farke kwallon.

Ofishin sashin Afrika na BBC- inda muke aiki ya rude da murna da tafi lokacin da Gervinho ya zira kwallo

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Mintuna 73 Colombia 2-Ivory Coast 1 - Gervinho

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Mintuna 69 Colombia 2-0 Ivory Coast - Juan Quintero. Wasa na neman kare wa ga, mummunan kariya daga 'yan bayan Ivory Coast

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Mintuna 68 Salomon Kalou ya karbi Max Griedel

Mintuna 66: Ivory Coast na ta kai farmaki amma har yanzu babu labari

Mintuna 64 James Rodriguez dan wasa ne kwararre kuma ya sanya wa kwallon kai da karfi bayan da Juan Cuadrado ya bugo kwana.

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Mintuna 64 Colombia 1-0 Ivory Coast - James Rodriguez

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Drogba ya karbi Bony

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Mintuna 55: An baiwa Didier Zokorakatin gargadi

Mintuna 53: Ivory Coast sun dawo da karfinsu inda Yaya Toure yake ta kaiwa da komowa a tsakiya.

Colombia 0-0 Ivory Coast 'yan wasa sun dawo fili a Brasilia.

Colombia 0-0 Ivory Coast

Ivory Coast sun kare wannan kashin da kwari amma duka bangarorin biyu za su ji cewa ya kamata ace sun zira kwallo.

Sueliman Dauda tsohon dan wasan Rachers Bees a Nigeria a BBC Hausa rediyo: Ya kamata Bony ya mike sosai idan har suna son su kai labari.

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

An tafi hutun rabin lokaci babu ci

Minti 45: Wasa ya kai wasa - kowa na kai kora.

Minti na 43: Colombia sun kai hari amma Zakora ya katse su kafin Ivory Coast suma su kece su kai wani harin.

Za ku iya sauraron sharhin a rediyo a kan mita 16 da kiloHerzt 17685 tare da Aminu Abdulkadir da Aliyu Tanko.

Mintina 35: Colombia 0-0 Ivory Coast kawo yanzu Colombia ne ke kai kora

Minti 31: 'Yan Ivory Coast na korafin yadda aka kayar da Yaya Toure amma ba a busa ba, sai dai nan kadan kuma sai Colombia suka samu bugun tazara

Minti 29: Colombia sun barar da kwallo mai kyau ta hannun Teofilo Gutierrez.Allah ne kawai ya tserar da Ivory Coast

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Hotunan talabijin sun nuna cewa yayi satar gida

Minti sama da 20 amma wasa na tafiya kowa na kara matsa kaimi, babu tabbas ko za mu samu kwallaye da yawa kamar yadda muka samu a wasannin da aka yi jiya.

Yusuf NNPC Gombe a shafinnu na BBC Hausa Facebook Ya Allah muna rokonka ka taimaki kashashen Afrika a wannan gasar, musamman Ivory Coast da Nigeria.

Minti 20 Colombia 0-0 Ivory Coast Colombia na kara matsa kaimi wurin kai kora, amma duka bangarorin biyu na taka leda sosai.

Minti 15 Colombia 0-0 Ivory Coast wasan a bude yake kowa na kai kora.

Aliyu Sulaiman Asheer ta shafin BBC Hausa Facebook To Kasar Ivory Coast da ma ku kadai muke saran za ku tabuka wani abin kirki. Sai ku dage kar ku bamu kunya.

Minti 10: Ivory Coast ta kai kora ta hannun Yaya Toure daga nan kuma Clombia suka yi zari-zuga amma basu yi nasarar kai labari ba.

17:11 Duka kasashen biyu sun kai kora, da farko Colombia sannan Ivory Coast - inda suka samu bugun kwana amma ta fita ba tare da wani hadari ba

17:08 Gutierrez na Colombia ya kai hari amma kwallon ta yi gefe sai dai ya tayar da hankalin 'yan bayan Ivory Coast.

17:07 Za ku iya bayyana ra'ayoyinku kan wasan ta shafukanmu na BBC Hausa Facebook ko taTwitter.

17:03 An fara wasa - kuma ciniki ya shiga

17:00 Yan wasa

Colombia: Ospina, Armero, Yepes, Zapata, Zuniga, Sanchez Moreno, Aguilar, Ibarbo, Rodriguez, Cuadrado, Gutierrez. Subs: Vargas, Arias, Carbonero, Guarin, Mejia, Balanta, Ramos, Quintero, Martinez, Valdes, Mondragon.

Ivory Coast: Barry, Boka, Bamba, Zokora, Aurier, Die, Tiote, Gervinho, Yaya Toure, Gradel, Bony. Subs: Gbohouo, Viera, Kolo Toure, Bolly, Akpa Akpro, Kalou, Drogba, Konan, Diomande, Djakpa, Sio, Sayouba.

Alkalin wasa: Howard Webb (England)

16:57 'Yan wasa sun fito fili ana yin taken kasashen biyu inda aka fara da na kasar Colombia.

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Magoya bayan Colombia a Brazil

16:50 Za ku iya sauraron sharhin a rediyo a kan mita 16 da kiloHerzt 17685.

16:48 Filin wasa ya dau harami magoya baya sai ihu suke yi da kade-kade

16:40 "Wannan babban wasa ne. Na kagu naga an fara taka leda tsakanin Colombia da Ivory Coast." a cewar mai gabatar da shirin wasanni na BBC kuma tsohon dan kwallon Ingila Gary Lineker

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Didier Drogba yana benci a tawagar Ivory Coast

16:34 Tawagar Ivory Coast: Barry, Boka, Zokora, Tiote, Gervinho, Bony, Gradel, Aurier, Y Toure, Die, Bamba.

16:30 Tawagar Colombia: Ospina, Zapata, Yepes, Sanchez, Armero, Aguilar, Gutierrez, Rodriguez, Cuadrado, Ibarbo, Zuniga.

16:30 Za ku iya bayyana ra'ayoyinku kan wasan ta shafukanmu na BBC Hausa Facebook ko ta Twitter.