David Rudisha zai fafata a Glasgow

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption David Rudisha ya dade yana fama da rauni

Zakaran tseren Olympics David Rudisha zai yi tsere a gasar Diamond League a birnin Glasgow a ranakun 11 da 12 ga watan Juli.

Wannan ne karon farko da dan tseren mai shekaru 25 dan kasar Kenya, zai fafata a Burtaniya tun bayan da ya kafa tarihi a mita 800 a gasar Olympic a London a shekara ta 2012.

Sauran 'yan tsere irinsu Shelly-Ann Fraser-Pryce da Carmelita Jeter na shirin shiga gasar da za a yi a Hampden Park.

Fraser-Pryce - daga Jamaica - wacce ita ce gwarzuwa a tseren mita 100 na duniya da kuma Olympic, na fama da rauni a kafa.