Alonso ya ce karshensu ya zo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alonso- farin ciki da nasarar da muka rika samu sun zo karshe.

Dan wasan tsakiya na Spain Xavi Alonso ya ce kaka-gidan da kasarsa ta yi a fagen kwallon duniya ya zo karshe bayan da aka fitar da su daga gasar a Brazil.

Kashin da Chile ta bai wa Spain mai rike da kofin na duniya da ci 2-0, bayan Holland ta lallasa su 5-1 na nufin zakarun Turan na 2012 ba za su iya fitowa ba daga rukuni na biyu,Group B.

Dan wasan na Real Madrid mai shekaru 32, ya ce ''watakila abin da ya fi shi ne a yi tunanin yadda za a yi sauye-sauye.''

Shi kuwa kocin Vicente Del Bosque wanda ya nuna alamun kawo karshen aikinsa na shekaru shida da kungiyar ta La Roja cewa ya yi, akwai abin da zai biyo bayan ficewar tasu daga gasar.

Kocin ya ce, ''ina ganin wannan tawagar 'yan wasan tana da kyau, amma dole ne mu dauki wani mataki kan abin da yake da kyau ga kwallon Spain kuma matakin har ni zai shafa.''