Costa Rica ta doke Italiya da ci 1 da 0

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bryan Ruiz ne ya ci wa Costa Rica kwallon

Costa Rica ta doke Italiya da ci daya mai ban haushi a wasan rukunin D na gasar cin kofin duniya da ake fafatawa da Brazil.

Wannan sakamakon ya tabbarwa Costa Rica gurbinta a zagaye na biyu na gasar.

Haka kuma tabbas Ingila ta fita kenan daga gasar, sannan kuma sakamakon wasa tsakanin Italiya da Uruguay ne zai tabbatar da kasar da za ta tsallake tare da Costa Rica a cikin rukunin.

Dan wasan Italiya, Mario Balotelli ya barar da dama sosai a wasan abinda 'yan kasar ke kuka da shi.

Wasan Costa Rica na karshe a rukunin zai kasance da Ingila ne a mako mai zuwa.