Nigeria za ta san matsayinta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Super Eagles sun ce harin da aka kai kan gidan kallo a Damaturu ya sa musu kishi

A wannan asabar ce kungiyar Super Eagles za ta kara da Bosnia-Herzegovina don tanatance matsayinta a gasar cin kofin duniya na Brazil.

Kungiyar tana bukatar yin nasara don ci gaba da kasancewa a gasar, bayan ta buga canjaras a wasanta na farko da Iran.

Rashin nasarar Super Eagles a wannan wasa zai sa ta dogara a kan wata kasa da kuma sakamakon wasanta na gaba a gasar, Bosnia kuma za ta fara tattara kayanta don komawa gida idan ta yi rashin nasara saboda a wasanta na farko Argentina ta lashe ta da 2 da 1.

Wasu sun soki kungiyar saboda gazawa wajen lallasa Iran, wadda aka fi ganin damarta a rukunin F.