Nigeria na gab da shiga zagaye na biyu

Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nigeria na gab da shiga zagaye na biyu

Peter Odemwingie ne ya zira kwallo daya tilon da ta baiwa Nigeria damar doke Bosnia-Hercegovina da ci 1-0 a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan na Stoke City ya zira kwallon ne a minti na 29 abinda ya baiwa Nigeria damar lashe wasa a karon farko a gasar tun shekara ta 1998.

Dan wasan gaba na Bosnia Edin Dzeko ya zira kwallo wacce alkalin wasa ya hana bisa kuskure mintina kadan kafin Nigeria ta zira kwallonta.

Nigeria za ta tsallake zuwa zagaye na gaba idan suka tashi canjaras da Argentina ko kuma idan Iran ta kasa samun nasara a kan Bosnia.

Karin bayani