Brazil ta lallasa Kamaru da ci 4-1

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Neymar ne ya zira kwallaye biyu

Brazil ta tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya bayan da ta lallasa Kamaru da ci 4-1 yayin da Mexico ta doke Croatia 3-1 duka a rukunin A.

Dan wasan Barcelona Neymar ne ya fara zira kwallo a minti na 17 kafin Joel Matip yafarke wa Kamaru a minti na 26.

Neymar ya sake zira kwallo ta biyu a minti na 34 kafin Fred ya zira ta uku da ka tare da taimakon David Luiz sannan Fernandinho ya zira ta hudu ana dab da tashi.

Brazil za ta kara da Chile a zagaye na biyu.

Ita kuwa Mexico za ta kara ne da Holland.

Ga yadda wasan ya gudana a sharhin da muka gabatar kai tsaye.

Da wannan muka kawo karshen wannan sharhi da muke kawo. Da fatan za a ci da kasancewa da bbchausa.com domin samun bayanai da dumi-duminsu a koda yaushe.

Wannan sakamako ya nuna cewa Brazil ta zamo ta daya a rukunin A yayin da Mexico ta zamo ta biyu. Kamaru da Croatia za su tattara kayansu domin komawa gida. Kamaru ce ta karshe a rukunin.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Magoya bayan Brazil na kallon wasan a allon majigi
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kamaru 1-4 Brazil

Minti na 93: Kamru sun kai kora amma kwalon ta fita kuma Julio Cesar ya yi bugun tazara.

Minti na 91: Brazil sun sake kai kora ta hannun Willian amma golan Kamaru ya cafke kwallon.

Croatia 1-3 Mexico

Mintina 87: Kamaru sun samu bugun tazara amma bai yi tasiri ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 84 Kamaru 1-4 Brazil Fernandinho da kafar hagu tare da taimakon Oscar

Croatia 0-3 Mexico

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Neymar yana da kwallo hudu kenan

Croatia 0-2 Mexico

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Salli (Kamaru)
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Brazil - Willian ya karbi Neymar

Mintina 66: Neymar yayi satar gida

Mintina 64: Kamaru na kai kora ta hannun Nkoulou

Croatia 0-0 Mexico a rukunin B

Mintina 60: (Brazil) ya yi laifi amma alkalin wasa bai hukunta shi ba kamar yadda aka yi tsammani

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kamaru: Salli ya shigo ya karbi Moukandjo

Mintina 57: Hulk ya yi kokarin kai kora amma bai yi tasiri ba.

Mintina 55: Wasa na hannun Brazil kawo yanzu ganin yadda suka kara zira kwallo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana nuna shakku kan kwallon da Fred ya zira ana ganin kamar yayi satar gida

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kamaru 1-3 Brazil Fred (Brazil) ya zira kwallo da ka da taimakon David Luiz

Mitnina 46: An dawo zagaye na biyu

Za ku iya sauraron sharhi kai tsaye a rediyo daga BBC Hausa a kan mita 25 da kiloHerzt 12060 tare da Aminu Abdulkadir da Aliyu Tanko.

Kashin farko Croatia 0-0 Mexico

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kamaru 1-2 Brazil - Neymar 17', 34' - Kamaru Matip 26

Minti 45: Hulk ya barar da dama mai kyau bayan da Neymar da Oscar suka yi wasa a tsakaninsu.

Minti 45: Amma an kara minti daya

Mintina 44: Moukandjo ya bugata ciki amma Brazil sun cire ba tare da matsala ba.

Mintina 43: Bugun tazara a wuri mai kyau ga Kamaru - David Luis ne ya jawo

Mintina 42: Silva ya tare hanzarin Kamaru na kai hari

Mintina 40: Kamaru 1-2 Brazil

Mintina 39: Mbiya (Kamaru) Ya kayar da Hulk na Brazil

Mintina 38: Alves (Brazil) ya janyo kwana amma Eyong Enoh ya buga kwallon waje bayan Kamaru sun bugo kwanar cikin sauri.

Mintina 35: Itandje (Kamaru) ya jawo kwana amma sun fitar da ita ba matsala.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mintina 34 Kamaru 1-2 Brazil - Neymar - ya narka kwallon da kafarsa ta dama

Mintina 33: Matip na Kamaru ya kara kai hari da ka amma kwallo ta fita waje.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mintina 26: Brazil 1-1 Kamaru - Joel Matip bayan Nyom ya taimaka masa

Mintina25: Matip na Kamaru ya kai hari da ka bayan an bugo kwana inda kwallon ta daki turke.

A yanzu Neymar ya zira kwallaye uku kenan a wasanni uku

Mintina 19: Neymar ya kara kai mummunan farmaki da kafarsa ta dama buga kwallon amma golan Kamaru Itandje ya ture ta da kyar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 16: Kamaru 0-1 Brazil ( Neymar) ya buga kwallon da kafarsa ta dama tare da taimakon Luiz Gustavo

Minti 14: An samu takaddama bayan dan wasan Kamaru ya ture Neymar a gefen fili, abinda ya harzuka 'yan wasa da magoya bayan Brazil.

Minti 13: Kamaru sun samu bugun tazara amma golan Brazil Julio Cesar ya cafke kwallon ba tare da matsala ba.

Mintina 12: Kamaru sun kai mummunar kora amma David Luis ya kwanta ya fitar da kwallon da kyar.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mintina 11: An baiwa Enoh (Kamaru) katin gargadi bayan ya tade Marcelo

Mintina 9: Kamaru sun kai kora amma Marcelo ya fitar da kwallon kwana - inda aka bugu amma suka cire ba tare da matsala ba.

Haka lamarin ya ke babu ci tsakanin Mexico 0-0 Croatia

Mintina 5: Brazil sun kai kora amma golan Kamaru ya cafke kwallon ba tare da matsala ba

Minti biyu: An kaiwa Kamaru mummunan hari amma sun fitar da ita kwana inda aka Neymar ya bugo kwanar amma suka kawar da ita cikin sauki.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan wasan Kamaru Samuel Eto'o ba zai taka leda ba, amma yana cikin masu baiwa sauran 'yan wasa kwarin gwiwa. Sai dai ya yi kwalliya kuam ya sha aski.

Minti daya: An fara wasa tsakanin Brazil da Kamaru

Tawagar Mexico: Ochoa, Rodriguez, Marquez (c), Herrera, Layun, Dos Santos, Moreno, Guardado, Peralta, Aguilar, Vazquez .

Croatia v Mexico (21:00 BST)

Tawagar Croatia: Pletikosa, Vrsaljko, Pranjic, Perisic, Corluka, Lovren, Rakitic, Modric, Srna, Mandzukic, Olic.

20:55 Tawagar Brazil: Julio Cesar, Dani Alves, Thiago Silva (c), David Luiz, Marcelo, Hulk, Paulinho, Fred, Neymar, Oscar, Luiz Gustavo

20:50 Kamaru v Brazil (21:00 BST)

Tawagar Kamaru: Itandje, Nkoulou (c), Nguemo, Moukandjo, Aboubakar, Bedimo, Choupo Moting, Mbia, Enoh, Matip, Nyom.

Za ku iya bayyana ra'ayoyinku kan yadda wasannin ke gudana a shafukanmu na BBC Hausa Facebook da kuma Twitter.

Za ku iya sauraron sharhi kai tsaye a rediyo daga BBC Hausa a kan mita 25 da kiloHerzt 12060 tare da Aminu Abdulkadir da Aliyu Tanko.