Bana son in bar Kamaru - Finke

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamaru ba ta taka rawar gani ba a Brazil

Kocin Kamaru, Volker Finke ya bayyana cewar yanason ya ci gaba da jan ragamar tawagar 'yan kwallon kasar duk da cewar an fitar da su daga gasar cin kofin duniya.

Tawagar Indomitable Lions ta sha kashi a wasanninta uku ciki hadda wasan da Brazil ta lallasa ta da ci hudu da daya a ranar Litinin.

Finke ya ce "Har yanzu kwangila ta, bata kare ba a wannan aikin".

Yanzu abinda zai mayar da hankali a kai shi ne tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin Afrika da za a fafata a badi.

A bisa yarjejeniya da ya kulla da hukumar kwallon Kamaru, akwai sauran shekara daya a kwangilar Finke na jan ragamar tawagar.

Karin bayani