Karin kudi ga 'yan wasan Ivory Coast

Karin kudi ga 'yan wasan Ivory Coast Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ivory Coast na kan hanyar tsallake wa zagaye na biyu

Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya ce zai ninkawa tawagar 'yan kwallon kasar kudin garabasar da ake basu idan suka doke Greece a wasan da za su yi a gasar cin kofin duniya.

Nasara a wasan kan zakarun Turai na shekara ta 2004 za ta baiwa Ivory Coast damar kaiwa zagaye na biyu.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ivory Coast ta bayyana a shafinta na internet cewa manufar ita ce "a kara wa 'yan wasan na Elephants kwarin gwiwa".

A yanzu ana baiwa kowanne daya daga cikin 'yan wasan dala $24,400 idan suka yi nasara - wanda yanzu zai karu zuwa $48,800.

Karin bayani