Mexico ta doke Croatia da ci 3-1

Mexico ta doke Brazil da ci 3-1 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mexico za ta kara da Netherlands a zagaye na biyu

Mexico ta kai zagaye na biyu inda za ta kara da Netherlands bayan da ta doke Croatia da ci 3-1 a rukunin A na gasart cin kofin duniya.

Rafael Marquez ne ya fara zira kwallo kafin Andres Guardado ya ci ta biyu sannan Javier Hernandez ya zira ta uku.

Ivan Perisic ne ya zira wa Croatia kwallon dayan da suka samu, sannan aka baiwa Ante Rebic jan kati.

Mexico sun taka rawar gani sosai kuma sun kare a matsayi na biyu da banbancin kwallaye kawai tsakaninsu da Brazil.

Karin bayani