Ingila da Costa Rica sun tashi 0-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ingila ta samu maki daya a wasanni uku

Ingila ta kamalla wasanninta uku a gasar cin kofin duniya ta bana ba tare da samun nasara ba, bayan da ta tashi babu ci tsakaninta da Costa Rica.

Kenan Ingila ce ta karshe a rukuni na hudu da maki daya.

Ingila ta saka sabbin 'yan wasa a karawar a yayinda Daniel Sturridge yake daga cikin manyan 'yan wasa biyu da suka buga duka wasannin kasar guda uku.

Wayne Rooney ya gwada gola, Keylor Navas amma kuma ya gamu da rashin nasara.

Kenan Costa Rica ce ta farko a rukunin D da maki bakwai, sai Uruguay ta biyu da maki shida, Italiya maki uku a yayinda Ingila keda maki daya.

Karin bayani