Djokovic ya tsallake zuwa zagaye na uku

Djokovic Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Novak Djokovic ya sha da kyar

Novak Djokovic ya kawar da kalubalen Radek Stepanek inda ya tsallake zuwa zagaye na uku na gasar Wimbledon.

Dan wasan na kasar Serbia wanda aka doke a wasan karshe na bara ya sha wuya kafin ya yi nasara da 6-4 6-3 6-7 (5-7) 7-6 (7-5).

"Mun yi horo tare kafin Wimbledon a don haka mun san juna," kamar yadda Djokovic ya shaida wa BBC.

Zakaran gasar Queen's Club Grigor Dimitrov shi ma ya tsallake.