Kocin Ivory Coast ya ajiye aiki

Image caption Kocin mai shekaru 42 ya ce, " 'Yan wasan sun ba da ni matuka."

Tsohon fitaccen dan wasan kasar Fransa kuma kocin kasar Ivory Coast Sabri Lamouchi, ya ajiye aikinsa na mai horar da 'yan wasa, bayan Ivory Coast ta kasa tsallake zagayen farko a gasar cin kofin duniya.

Kungiyar ta Elephant ta yi rashin nasara a hannun Greece a wasan da suka yi ranar Talata bayan da aka kammala wasan da ci 2-1, inda Ivory Coast ta tsaya a matsayin ta uku yayin da abokiyar karawarta ta ke matsayi na hudu a rukunin C.

Kwantiragin kocin Sabri Lamouchi zai kare ne a karshen gasar cin kofin duniyar da ake yi a Brazil.

Kocin mai shekaru 42 ya ce, " 'Yan wasan sun ba da ni matuka."

Da ace an tashi wasan canjaras tsakanin Ivory Coast da Greece da Ivory Coast din ta kai ga zagaye na biyu, amma hakan bai samu ba.