Girka ta cire Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto Getty

Girka ta cire Ivory Coast daga gasar cin kofin duniya, duk da zaton tsallaka wa zagaye na gaba da aka yi wa kasar ta nahiyar Afirka tun da farko.

Georgios Samaras ne ya zura kwallon da ta dinke nasarar Girka a wani bugun fanareti mai takaddama, inda wasa ya kaya 2 da 1.

Girka ce ta fara jefa wa Ivory Coast kwallo a farkon rabin lokaci ta hannun Andreas Samaris sakamakon kuskuren Dan bayan Ivory Coast, Cheick Tiote.

Daga bisani Ivory Coast ta farke inda ta samu maki 1 da take bukata zuwa zagayen gaba amma a karshe wasa ya kaya, Girka ta kafa tarihin zuwa zagayen sili daya kwale a karon farko da maki hudu.

Girka dai a yanzu za ta kara ne a zagaye na gaba da Costa Rica ta sama a rukunin D, ranar lahadi