Za a binciki tawagar kwallon Kamaru

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamaru ce kasa ta farko da aka fara fitarwa a karon farko

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya yi kira da a gudanar da bincike kan mummunar rawar da kasar ta taka a gasar cin kofin duniya.

Tawagar Indomitable Lions basu taka rawar gani ba bayan da suka sha kayi a dukka wasanninsu uku, an basu jan kati, kuma 'yan wasansu sun yi fada da juna a cikin fili.

An zirawa Kamaru kwallo

tara, sannan suka zira daya tilo kuma su ne na farko da aka fara fitarwa daga gasar.

An umarci Fira Minista Philemon Yang da ya fara gudanar da bincike kan abubuwan da suka haifar da matsalar.

Kamaru ta sha kayi a hannun Mexico da ci 1-0 a wasanta na farko a rukunin A, sannan Croatia ta doke ta da ci 4-0 kafin Brazil ta lallasa ta da ci 4-1.

Karin bayani