Manchester City sun sayi Fernando

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Zan sadaukar da lokaci na a kowane wasa, ina kuma fatan samun farin ciki a zaman da zan yi a Man City.'

Kungiyar Manchester City ta kammala cinikin dan wasan gaban Brazil Fernando da ke taka leda a FC Porto.

Kulob din na kasar Portugal ya bayyana batun cinikin dan wasan a wajen hada-hadar kasuwancin hannun jari na Lisbon ranar Laraba, bayan kulla yarjejeniya da City din kan kudi fam miliyan 12.

Man City ta tabbatar da cinikin dan wasan mai shekaru 26 ranar Alhamis, sai dai ba a bayyana adadin tsawon lokacin kwantiragin na sa ba.

Fernando ya ce, "Na yi matukar farin ciki da kasancewa a Man City, na san tun cikin watan Janairu ake maganar cinikina, saboda haka na ji dadi da ganin cinikin ya tabbata a yanzu na zama dan wasan kulob din City."