Kai tsaye: Ghana da Portugal

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan shafi zai kawo muku sharhi kai tsaye kan wasan Ghana da Portuga, Jamus da Amurka a rukunin G na gasar cin kofin duniya. Latsa nan domin samun sabbin bayanai.

Mun kawo karshen sharhin da muke kawo muku na wasan Ghana da Jamus. Sai a ci gaba da kasancewa tare da bbchausa.com domin samun cikakkun labarai.

Ra'ayoyi daga shafin BBC Hausa Facebook:

Adam A Adam Gashua -To 'yan wasan Afrika sai ku kara zage dantse don ganin kun cire mana kitse daga wuta

Muhammad Abdulmalik-Haba: Ghana daga yanzu anya kuwa za ku tabuka abun kirki kuwa?

Yusuf NNPC Raypower Gombe - Ghana kun ba mu kunya da kuka ci kan ku da kan ku.

Jami'an Portugal na ta lallashin Ronaldo - har lokacin da ya fice daga fili.

An tashi wasa Ghana -1-2 Portugal - Amurka 0-1 Jamus

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Moutinho (Portugal) bayan ya tade Gyan.

Bugun tazara a wuri mai kyau ga Ghana Moutinho ne ya tade Gyan (Ghana).

Ronaldo ya sake kai kora amma Dauda - golan Ghana ya hanashi.

Golan Portugal Veto da aka cire yana ta kuka.

An kara minti hudu

Gyan - Ghana ya kai kora da kafar hagu sai dai kwallo ta fita waje.

Ghana sun kai kora amma golan Portugal ya cafke kwallon.

Kwana ga Ghana - sun bugo amma ta fita ba matsala ga Portugal

Ronaldo ya sake kai kora amma golan Ghana Dauda ya ture kwallon.

Ghana sun kai kora amma kwallo ta fita.

Hakkin mallakar hoto AFP
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ghana 1-2 Portugal - Ronaldo da kafar hagu bayan golan Ghana ya yi amai.

Ghana -1-1 Portugal - minti 79

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption J Ayew (Ghana)

Jordan Ayew - Ghana ya buga kwallo da kafar hagu amma ta yi waje.

Portugal sun bugu kwana amma golan Ghana ya ture ta.

Amurka 0-1 Jamus - Muller minti - 55

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jordan Ayew (Ghana) ya karbi Warris

Ronaldo - Portugal ya bugo kwallo daga bangaren hagu amma babu kowa a cikin 'yan Portugal.

Verela (Portugal) ya kai kora amma kwallon ta yi sama sosai ba matsala ga Ghana.

Alves (Portugal) ya ture Gyan - bugun tazara ga Ghana.

Anm hadu tsakanin Ronaldo da Dauda - amma ance Ronaldo ya yi laifi.

Warris - Ghana ya barar da dama mai kyau - ya sa kai bayan da Gyan ya bugo masa kwallon daga bangaren hagu.

Kwana ga Portugal - amma golan Ghana Dauda ya kama kwallo.

Hakkin mallakar hoto Getty
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ghana 1-1 Portugal - Gyan Ghana da ka tare da taimakon Asamoah
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Warris na Ghana bayan ya taka Pepe (Portugal)

Warris - Ghana ya yi laifi

An fara kashi na biyu wasa

Karin bayani: Labarin da muke samu na cewa Uruguay za ta daukaka kara kan dakatarwar da aka yi wa dan wasanta Luis Suarez na wasanni tara da kuma watanni hudu daga dukkan harkokin kwallon kafa.

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ce ta same da laifin cizon dan wasan Italiya Giorgio Chiellini.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An tafi hutun rabin lokaci Ghana 0-1 Portugal. Amurka 0-0 Jamus

Saura kiris Boye - Ghana ya kara cin gida bayan an bugo wa Ronaldo kwallo .

Gyan - Ghana ya nemi fanareti a jikin Alves amma alkalin wasa bai saya ba.

Portugal sun kai hari amma Dauda - golan Ghana ya kama kwallon bayan an bugota daga bangaren dama.

Amurka 0-0 Jamus - Sakamakon wannan wasa shi ne zai nuna makomar Portugal da Ghana koda daya daga cikinsu ya yi nasara.

Atsu - Ghana ya kai kora amma kwallon ta bude ta fita ba matsala.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Afful na Ghana saboda ya doke Ronaldo

Asamoah - Ghana ya yi laifi - bugun tazara ga Portugal.

Gyan - Ghana ya kai hari amma kwallo ta fita.

Pereira - Portugal ya kai hari da kafar dama amma kwallon ta fita ta kusa da turken ragar Ghana.

Ronaldo - Portugal ya kai mummunan hari da karfi da kafar dama amma golan Ghana ya ture kwallon da kyar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 30 Ghana 0-1 Portugal - Boye (Ghana) ya ci gida bayan an bugu kwallo daga hannun hagu.

An bugo kwanar amma Portugal sun fitar ba tare da matsala ba.

Ghana sun samu kwana - Alves ne ya fitar da kwallon.

Portugal sun kai kora ta hannun Veloso amma golan Ghana Dauda ya cafke kwallon.

An yi wa Ronaldo laifi - amma sun buga cikin sauri inda kuma kwallo ta lalace.

Kwana biyu daga Ghana amma kwallo ta koma hannun Portugal

Ghana sun kai kora ta hannun Asamoah amma kwallon ta fita kwana.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu magoya bayan Ghana a Brazil

Ghana sun samu bugun tazara - Cavalho ne ya yi laifin.

Gyan - Ghana ya kai kora amma golan Portugal ya tare kwallon.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ronaldo - Portugal ya kai mummunan hari da ka inda Dauda ya tare kwallon - saura kiris

Gyan na Ghana ya samu dama a yadi na 18 na Portugal amma Portugal sun kwace kwallon.

Moutinho na Portugal yayi laifi

Ghana sun kai kora amma kwallon da Gyan ya bugo ta fada hannun golan Portugal Beto.

Minti 10: Mai tsaron gidan Ghana Dauda ya ture kwallon ta fita kwana bayan bugun da Ronaldo yayi da kafar dama.

Minti 8: Ronaldo ya samu bugun tazara a wuri mai hadari ga Ghana.

Minti 6: João Pereira (Portugal)ya samu bugun tazara.

Ronaldo (Portugal) ya kai kora inda kwallo ta daki turki.

An fara wasa Ghana 0-0 Portugal

Tawagar Jamus: Neuer, Howedes, Hummels, Schweinsteiger, Ozil, Podolski, Muller, Lahm (c), Mertesacker, Kroos, Boateng

Tawagar Amurka: Howard, Gonzalez, Bradley, Besler, Beasley, Dempsey (c), Jones, Davis, Beckerman, Zusi, Johnson

Tawagar Ghana: Dauda, Gyan (c), Atsu, Agyemang Badu, A. Ayew, Rabiu, Waris, Mensah, Asamoah, Boye, Afful

Tawagar Portugal da za ta kara da Ghana: Beto, Bruno Alves, Pepe, Miguel Veloso, William Carvalho, Ronaldo (c), Moutinho, Eder, Nani, Amorim, Pereira

16:48 Batun korar Sulley Muntari da Kevin-Prince Boateng saboda zargin rashin da'a ya mamaye shirinsu na wasan.