'Messi daga duniyar Jupita ya ke'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Keshi ya gode wa 'yan wasan da magoya baya da wasu daga cikin kafafan yada labarai.

Kocin Nigeria Stephen Keshi ya ce dan wasan Argentina Loinel Messi daga duniyar Jupita ya fado saboda yadda ya burge shi a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan mai shekaru 27 ya jefa kwallaye biyu a ragar Najeriya ta hanyar tashi sama da bugun tazara wanda hakan ya bai wa Argentina damar samun matsayi na daya a rukunin F.

Keshi wanda kungiyarsa ta yi nasarar tsallakewa zuwa zagaye na biyu, duk da rashin nasarar da ta yi a wasansu da Argentina, cewa ya yi "Messi dan wasa ne na daban, ya kuma samu tabarraki, ba za ka iya kushe shi ba."

Ya kuma kara da cewa, "Akwai zaratan 'yan wasa a Argentina sai dai Messi ya fita daban."