An dakatar da Suarez wasanni tara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne karo na uku da Suarez ya yi cizo a kwallon kafa

An dakatar da dan wasan Uruguay Luis Suarez wasanni tara bayan an same shi da laifin cizon dan wasan Italy Giorgio Chiellini.

An kuma hana dan wasan shiga duk wasu al'amuran kwallon kafa na tsawon watanni hudu.

"Kwamitin ladaftarwa na Hukmar kwallon kafa ta duniya Fifa ya yanke shawara cewa dan wasan ya saba kundin na 48 da na 57 na dokokinta, a don haka ta yanke hukuncin dakatar da shi wasanni tara", a cewar manajan yada labarai na Fifa Delia Fischer.

Wanann na nufin Suarez ba zai buga wasan da Uruguay za ta yi da Colombia ba a ranar Asabar.

Wakilin BBC na fannin wasanni Richard Conway, ya ce Suarez ka iya daukaka kara, amma Fifa ta ce koda ya daukaka karar dakatarwar za ta ci gaba da aiki.

Hakan na nufin cewa ba zai sake taka leda a gasar cin kofin duniya ta bana ba.