Barcelona na neman Suarez

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Suarez ya shiga bakin duniya tun bayan abinda ya faru

Barcelona sun na ce kan bukatarsu ta neman sayen dan wasan Uruguay Luis Suarez duk da dakatarwar da aka yi masa na watanni hudu kan cizon Giorgio Chiellini.

Dan wasan na Liverpool mai shekaru, 27, ba zai iya shiga wata harkar kwallon kafa ba har sai karshen watan Oktoba.

Suarez ya ciji Chiellini a wasan da Uruguay da doke Italy da ci 1-0 wanda ya basu damar tsallake wa zuwa zagaye na biyu.

An fahimci cewa kulob din na La liga, wadanda ke da Neymar da Lionel Messi, za su yi yunkurin sayen Suarez idan suka same shi a farashin da ya dace da aljihunsu.

Karin bayani