Wimbledon 2014: Djokovic ya doke Simon

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Novak Djokovic shi ne na biyu a duniya

Novak Djokovic ya tsallake zuwa zagaye na hudu na gasar Tennis ta Wimbledon bayan da ya doke Gilles Simon 6-4 6-2 6-4 na Faransa.

Dan wasan na Serbia ya samu rauni a zagaye na uku na wasan bayan da ya fadi a kan kafadarsa ta hagu, amma bayan hakan komai ya tafi daidai.

Djokovic wanda shi ne na biyu a duniya zai kara da Jo-Wilfried Tsonga a wasa na gaba bayan da dan Faransar ya doke Jimmy Wang 6-2 6-2 7-5.

Kevin Anderson na Afrika ta Kudu ya doke Fabio Fognini a zagaye biyar.

Karin bayani