Kofin duniya: Brazil ta fitar da Chile

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Brazil ta kai wasan dab da na kusa da na karshe

Brazil ta fitar da Chile daga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, a bugun fanareti, bayan cikar wa'adin wasan ba tare da wata ta yi galaba ba

Bayan mintuna casa'in na wasan kowacce tana da ci daya.

Bayan mintuna talatin din da aka kara masu, ba ta sauya zani ba, shi ne aka yi bugun fanareti, inda Brazil ta yi nasara da ci 4 da 3.