Nigeria, Algeria: Ina makomar Afirka?

Stephen Keshi
Bayanan hoto,

Kocin Nigeria, Stephen Keshi, ya ce shi da 'yan wasansa suna daukar ko wanne wasa tamkar final

A wasanni biyun da za a buga na Gasar Cin Kofin Duniya a Brazil ranar Litinin, tawagogin Afirka biyu da suka rage ne za su yi gwagwarmayar samun gurbi a quarter finals.

A wasa na farko Nigeria za ta fuskanci Faransa, yayin da a wasa na biyu, Jamus za ta kece raini da Algeria.

Wani abin albishir ga tawagar Najeriya dai shi ne cewa Victor Moses, wanda bai buga wasan kasarsa da Argentina ba sakamkon raunin da ya yi ya koma fili, inda ya yi atisaye da 'yan uwansa.

Magoya bayan Super Eagles dai na fatan 'yan wasan tawagar za su mai da hankali sosai duk da raunin da suke da shi a baya, da fatan kocinsu zai sanya 'yan wasan da suka dace a lokacin da ya dace.

Shi dai kocin Nigeriar, Stephen Keshi, cewa ya yi samun gurbi a zagaye na biyu na gasar ma babbar nasara ce ga tawagar: "Ina ganin babbar nasara ce saboda idan ka duba rabin tawagogin da suka zo nan sun koma gida, amma mu muna nan tare da wasu daga cikin tawagogin da suka fi kwazo a duniya; ga shi kuma a shekaru 16 da suka wuce Nigeria ba ta samu isa zagaye na biyu na Gasar Cin Kofin Duniya ba.

Dangane da 'yan wasan Faransa kuma sai Keshi ya ce: zakakuran 'yan was ne, don haka za mu fafata da su bil hakki kamar yadda muka yi da Argentina, da Bosnia, da sauransu.