Super Eagles za su fafata da Faransa

Super Eagles na Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan Super Eagles na fatan samun nasara a wasa da Faransa.

'Yan wasan Super Eagles na Nigeria za su fafata da kasar Faransa ranar Litinin, don neman samun gurbi zuwa quarter finals a Gasar cin Kofin Duniya a Brazil.

Wani abin albishir ga tawagar Najeriyar shi ne cewa Victor Moses, wanda bai buga wasan kasar da Argentina ba sakamakon raunin da ya samu, yanzu ya warke kuma har ma ya yi atisaye da 'yan uwansa.

Magoya bayan Super Eagles na fatan 'yan wasan za su mai da hankali sosai duk da raunin da suke da shi a baya tare da fatan kocin su zai sanya 'yan wasan da suka dace a wasan.

Mai horar da 'yan wasan Najeriyar, Stephen Keshi, ya ce samun gurbi a zagaye na biyu na gasar da 'yan wasan Super Eagles suka yi babbar nasara ce ga tawagar.