Kai tsaye: Nigeria da Faransa

Kai tsaye: Nigeria da Faransa Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan shafi na kawo muku sharhi kai tsaye kan wasan zagayen 'yan 16 tsakanin Nigeria da Faransa a gasar cin kofin duniya. Latsa nan domin samun sabbin bayanai.

Mun kawo karshen wannan sharhi da muke kawo muku. Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare da bbchausa.com akoda yaushe domin samun cikakkun bayanai.

Ra'ayoyi daga shafin BBC Hausa Facebook: Saminu Hamisu: Babu komai mun fi Spain Italy, England,Croatia, Ivory coast, Ghana da sauransu.

Mubarak Shuaibu Dukawa: Hah hah hah wallahi naji dadi sosai ayo gidan gado ko? Up France kun burgeni me za a yi da Nigeria.

Luka Balarabe: Gaskiya 'yan wasan sun yi abin yabo kuma sun haska Nigeria a idon duniya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Faransa Francois Hollande yana murna a fadarsa ta Elysee lokacin da kasarsa ta zira kwallo a ragar Nigeria.

Sharhi: Ina ganin Nigeria za su yi takaici idan suka koma suka kalli yadda wasan ya gudana saboda kuskuren da suka yi na rashin amfani da damar-makinsu". Tsohon dan wasan Ingila da Machester United Rio Ferdinand.

Hakkin mallakar hoto AFP

Yanzu Nigeria sai gida kenan. Fatan Afrika ya rage a kan Algeria wacce za ta kara da Jamus da misalin karfe 9.00 na dare.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An tashi wasa Nigeria 0-2 Faransa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 90+2 Nigeria 0-2 Faransa - Yobe (Nigeria) ya ci gida. Bayan an bugo kwana a hankali.

An kara minti biyar Nigeria 0-1 Faransa

Minti 89: Faransa sun samu kwana ta hannun Pogba bayan da Oshinawa ya fitar da ita.

Minti 88: Faransa sun samu bugun tazara - Nigeria ba sa taka leda yadda ya kamata.

Minti 87: Nigeria 0-1 Faransa - duk wanda ya yi nasara zai hadu da wanda ya doke wani tsakanin Jamus da Algeria.

Hakkin mallakar hoto AFP

Minti 85: Moses ya samowa Nigeria kwana.

Minti 83: Griezmann (Faransa)ya kai mummunar kora amma Enyeama ya fitar da ita kwana da kyar.

Wannan ce kwallo ta uku da Paul Pogba ya zira a Faransa - kuma ita ce ta farko a gasar cin kofin duniya.

Da ma Faransa sun matsa da kai kora - don haka kwallon bata zo da mamaki ba.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption NIgeria 0-1 Faransa - Pogba da ka, bayan Enyeama ya yi kuskure

Minti 78: Benzema ya sake kai kora amma Enyeama ya fitar kwana.

Minti 77: Nigeria sun sake sha da kyar. Wannan karon Cabaye ne ya kai kora, kwallon farko ta wuce kowa amma Ambrose ya cire ta. Yayin da ta biyu ta daki turke.

Minti 75: Faransa sun kai kora amma kwallo ta fita kwana. An bugo ta sake fita kwana bayan da Koscielny ya sa kai.

Labari da dumi-dumi: Luis Suarez ya nemi afuwa abisa cizon da yayi wa Giorgio Chiellini na Italiya. A bayanin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Suarez ya yi alkawarin "ba zai sake yin halayya irin wannan ba".

Minti 69: Nigeria sun sha da kyar - Moses ya cire kwallon bayan ta wuce kowa. Benzema ne ya kai korar inda kwallon ta wuce Enyeama. Wannan ne hario mafi muni.

Hakkin mallakar hoto AFP

Minti 68: Nigeria sun kai kora ta hannun Musa amma Koscielny ya fitar da kwallon kwana - wacce Faransa suka fitar ba matsala.

Minti 66: Faransa sun kai kora amma Oshinawa ya fitar da kwallon da kyar bayan Enyeama ya taba kwallon.

Minti 64: Nigeria ta sake kai kora ta hannun Odemwingie da kafar hagu amma Loris ya ture kwallon da kyar.

Minti 63: Nigeria sun kai kora ta hannun Odemwingie amma babu kowa kwallo ta fita.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 61 Griezmann (Faransa) ya karbi Giroud
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Reuben Gabriel (Nigeria) ya karbi Onazi wanda ya samu rauni

Minti 57: Kwana ga Nigeria - Odemwingie ya bugu amma Faransa sun cire.

Onazi (Nigeria) ya samu rauni kuma an fitar da shi. Da alamu raunin na da tsanani.

Hakkin mallakar hoto AFP

Minti 56: Nigeria 0-0 Faransa

An dawo zagaye na biyu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Suma Faransa haka - na da magoya baya
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria sun samu goyon baya sosai kafin a fara wasan

Ra'ayoyi daga shafin BBC Hausa Facebook: Abubakar Sadiku Abubakar: Muna jiran yan wasar Nigeria a filin jirgin abuja yau-yau din nan domin ba za su iya ba!!!

Nigeria 0-0 Faransa: Dukka bangarorin biyu sun kai kora. Ba mamaki mu kai bugun fanareti, da fatan sun yi horo sosai. Da alamu kocin Faransa Didier Deschamps ne zai fi damuwa a tsakanin kociyoyin biyu.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An tafi hutun rabin lokaci: Nigeria 0-0 Faransa

Minti 45+2 Onazi (Nigeria) ya yi laifi. Bugun tazara ga Faransa - an bugo amma 'yan Faransa sun yi laifi.

Minti 45+1Matuidi (Faransa) yature Moses amma kwallo ta fita an ce babu komai.

Minti 43: Emenike (Nigeria) ya kai kora daga wajen yadi na 18 amma Loris ya ture kwallon da kyar.

Minti 39: Matuidi (Faransa) ya kai mummunar kora amma kwallo ta fita.

Minti 38: Nigeria sun bugo kwana ta hannun Musa amma ta wuce kowa ta fita. Bugun tazara ga Faransa.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria 0-0 Faransa

Ra'ayoyi daga shafin BBC Hausa Facebook: Aliyu B Liman Nigeria za su lallasa Farance da ci biyu 2 -0 insha Allahu. Sai mun hadu za'a banbance tsaki da tsakuwa.

Minti 31: Faransa sun samu kwana amma kwallo ta fita jefa ga Faransa.

Minti 30: An bugo kwana amma Odemwingie ya ture Loris.

Minti 29: Odemwingie ya tattaba kwallo da Emenike amma 'yan Faransa sun fitar da ita. Kwana ga Nigeria.

Minti 28: Valbuena (Faransa) ya yi laifi.

Minti 27: Yobo (Nigeria) ya fitar da korar da Faransa suka kawo ta hannun Benzema.

Minti 25: Nigeria sun samu kwana ta hannun Evra( Faransa).

Hakkin mallakar hoto AFP

Za ku iya bayyana ra'ayoyinku kan yadda wasannin ke gudana ta shafukanmu na sada zumunta kamar BBC Hausa Facebook ko Twitter.

Minti 24: Nigeria sun bugo kwana amma golan Faransa Loris ya cafke kwallon.

Minti 21: Faransa sun kai mummunan hari ta hannun Pogba da kafar hagu amma Enyeama ya ture kwallon zuwa kwana. An bugu kuma ta fita ba matsala.

Hakkin mallakar hoto Getty

Minti 20: Nigeria 0-0 Faransa - Faransa sun kai kora amma ance Benzema ya yi satar gida.

Minti 18: Nigeria sun zira kwallo ta hannun Emenike amma alkalin wasa ya hana saboda an yi satar gida.

Minti 17: Emenike ya buga kwallon sama. Ba karamar dama ya zubar ba saboda bugun tazara ne mai kyau.

Minti 15: Nigeria sun kara samun bugun tazara a wuri mai kyau bayan da aka tade Odemwingie.

Minti 14: Nigeria sun yi bugun tazara amma golan Faransa ya kame kwallon.

Minti 13: An fitar da Nigeria Onaze bayan da fadi lokacin da ya hadu da Pogba (Faransa).

Minti 12: Nigeria ta samu bugun tazara daga gefen ragar Faransa, bayan da Cabaye ya tade dan Nigeria Emenike.

Minti 10: Nigeria 0-0 Faransa - Nigeria na rike kwallo suna tattaba ta.

Minti 6: Nigeria ta kai kora amma Odemwingie bai take kwallon yadda ya kamata ba, 'yan Faransa sun fitar da ita babu matsala.

Minti 4: Faransa sun kai hari amma Yobo ya fitar da kwallon kwana - kuma an bugo amma ta yi waje ba tare da matsala ba. Bugun tazara ga Nigeria.

Minti 3 Nigeria ta samu kwanar farko a wasan ta hannun Koscielny (Faransa) amma sun fitar da kwallon.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tawagar Faransa loris, Debuchy, Evra, Koscielny, Varane, Cabaye, Valbuena, Benzema, Matuidi, Pogba, Giroud.
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tawagar Nigeria: Enyeama; Ambrose, Yobo, Oshaniwa, Omeruo; Onazi, Mikel; Musa, Odemwingie, Moses; Emenike.

An fara wasa Nigeria 0-0 Faransa

16.59 Dan wasan Nigeria Joseph Yobo zai kafa tarihi inda zai buga wasa na 100 a Nigeria - shi ne na farko da ya cimma wannan matsayi.

16.57 'Yan wasa sun fito fili inda aka yi taken kasashen biyu: Nigeria da Faransa.

16:49 A karon farko a tarihi an samu kasashen Afrika guda biyu da suka kai zagaye na biyu a lokaci guda: Nigeria da Algeria.

16.47 Rawa mafi kyau da kasashen Afrika suka taka a gasar cin kofin duniya ita ce ta zuwa zagayen daf da na kusa da na karshe: Cameroon (1990), Senegal (2002) da kuma Ghana (2010).

16.45 Kocin Nigeria Stephen Keshi: Ina matukar alfahari da rawar da na taka kuma ina so na dora kan abinda na riga na cimma.

16.43 Labarin da muka samu yanzu na cewa Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya Fifa ta dakatar da daraktan yada labarai na Brazil, Rodrigo Paiva, har sai an kammala binciken da ake gudanarwa a kansa. An zarge shi da yunkurin dukan dan wasan Chile Mauricio Pinilla a lokacin da kasashen biyu suka kara.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sabanin Nigeria - da aka samu sabani kan batun kudaden garabasa, babu makamancin wannan rudanin a tawagar Faransa.

16.36 Tawagar Faransa loris, Debuchy, Evra, Koscielny, Varane, Cabaye, Valbuena, Benzema, Matuidi, Pogba, Giroud.

16.32 Tawagar Nigeria da za ta kara da Faransa: Enyeama; Ambrose, Yobo, Oshaniwa, Omeruo; Onazi, Mikel; Musa, Odemwingie, Moses; Emenike.

16.30 Wannan ne karo na farko da Nigeria ta kai zagaye na biyu tun 1998.

Karin bayani