Brazil 2014: Faransa ta fitar da Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan ce kwallo ta uku da Paul Pogba ya zira a rayuwarsa ta Faransa

An fitar da Nigeria daga gasar cin kofin duniya bayan da Faransa ta doke ta da ci 2-0. Pogba ne ya zira kwallon farko yayin da Yobo ya ci gida.

Emmanuel Emenike na Nigeria ya zira kwallo amma aka hana saboda an yi satar gida kafin Vincent Enyeama ya kawar da mummunan harin da Pogba ya kai.

Shi ma Victor Moses ya fitar da harin da Karim Benzema ya kai bayan kwallon ta wuce kowa sannan Yohan Cabaye ya daki turke.

Pogba ya zira kwallon farko bayan kuskuren da Enyeama ya yi, kafin Yobo ya ci gida sakamakon kwallon da Mathieu Valbuenas ya bugo bayan an yi kwana.

Faransa za su kara da wanda ya samu nasara tsakanin Jamus da Algeria.