Luis Suarez ya nemi afuwar Chiellini

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Suarez ya samu kyakkyawar tarba lokacin da ya koma gida

Dan wasan Liverpool Luis Suarez ya nemi afuwar Giorgio Chiellini game da cizon da yayi masa wanda ya sa aka dakatar da shi wasanni tara da kuma watanni hudu daga al'amuran kwallon kafa.

An dakatar da dan kwallon na Uruguay, mai shekaru 27, daga kwallon kafa saboda cizon da ya yiwa dan bayan Italiya Chiellini a gasar cin kofin duniya.

"Gaskiya ita ce abokin wasa na Giorgio Chiellini ya ji radadin cizon da na yi masa," a cewar Suarez, a wata sanarwa da ya fitar.

Da farko Suarez ya musanta lamarin inda ya ce zame wa yayi kuma bai ciji Chiellini ba. Amma a shafinsa na Twitter, Suarez ya yi alkawarin "ba zai sake yin halayya irin wannan ba".

Wannan ne karo na uku da aka dakatar da Suarez bayan da a baya ya ciji dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic a 2013 da kuma dan PSV Otman Bakkal a 2010.

Karin bayani