Kamaru za ta binciki batun cogen wasa

'Yan wasan Kamaru Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamaru ta yi rashin nasara a dukkan wasanninta a gasar cin kofin duniya a Brazil

Jami'ai a Kamaru sun ce za su gudanar da bincike kan ikirarin cewa akwai hannun 'yan wasan kasar su bakwai a cogen wasa na gasar cin kofin duniya a Brazil.

Kwamitin tabbatar da da'a na Hukumar kwallon kafa ta Kamaru ne zai gudanar da bincike a kan ikirarin aikata zamba a wasannin da kasar ta buga a matakin rukuni a gasar.

A wata hira da ya yi da wata mujallar kasar Jamus mai suna Der Spiegel, mutumin nan da 'yan sanda ke tsare da shi a kasar Finland,Wilson Raj Perumal kan zargin cogen wasa ya yi hasashen da ya zama gaskiya a wasan Kamaru da Croatia kuma ya ce za a kori dan wasan Kamaru daga wasa.

Yayin gasar cin kofin duniya, Kamaru ta yi rashin nasara a dukkan wasanninta a rukunin A, ciki har da wasan data buga da Croatia inda aka lallasa ta ci 4 da nema.