Adam Lallana ya koma Liverpool

Adam Lallana Hakkin mallakar hoto Liverpool
Image caption Lallana ya yi wa Ingila wasa a gasar cin kofin duniya a Brazil

Kyaftin din Southampton Adam Lallana ya kammala shirye-shiryen komawa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool daga Southampton kan kudi fam miliyan 25.

Lallana mai shekaru 26, shi ne dan wasa na biyu da kocin na Liverpool ya dauka a kakar wasa ta bana tare da Rickie Lambert.

Lallana wanda dan wasan tsakiya ne da ya yi wa Ingila wasa a gasar cin kofin duniya da ake yi a Brazil, ya kuma buga wa Saints wasanni 265.

Dan wasan ya ce "Na yi matukar farin ciki wannan ci gaba da na samu da zuwa na fitaccen kulob na Liverpool."

Ya kuma kara da cewa, yana fatan zai taimaka wa kulob din wajen cin kyaututtuka domin a cewar sa, wannan shi ne makasudin komawarsa Liverpool.