Argentina ta fitar da Switzerland

Image caption Di Maria ne ya raba gaddama a minti na 118.

Argentina ta samu galaba a kan kasar Switzerland a wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da ci daya mai ban haushi.

Angel Di Maria shi ne ya ci kwallon a cikin karin lokacin bayan da suka tashi babu ci a cikin mintuna 90.

Da kyar Argentina ta ci kwallon, bayan da golan Switzerland, Diego Benaglio ya kabe hare-haren da Lionel Messi da kuma Gonzalo Higuan suka yi ta kai wa.

Kenan Argentina ta tsallake zuwa zagayen gabda na kusada karshe wanda za ta buga a ranar Asabar mai zuwa.

Karin bayani