Klinsmann ya caccaki FIFA

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Klinsmann na murnar kaiwa zagaye na biyu

Kocin tawagar 'yan kwallon Amurka, Jurgen Klinsmann ya soki Fifa saboda nada alkalin wasa dan kasar Algeria a matsayin wanda zai jagoranci wasansu da Belgium.

Djamel Haimoudi mai shekaru 44, shi ne alkalin wasa a karawar da za a yi a Salvador a ranar Talata.

Klinsmann ya ce 'yan wasan Belgium za su iya zantawa da alkalin wasan saboda sun iya magana da harshen Faransanci.

Ya ce "Akwai matukar wuya in fahimci dalilan Fifa na zabar alkalin wasa".

Amurka za ta kece raini da Belgium da karfe takwas agogon GMT.

Karin bayani