Neymar zai buga wasansu da Colombia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Neymar ba zai shiga horo ba

Bisa dukkan alamu, dan kwallon Brazil Neymar zai buga wasansu da Colombia a ranar Juma'a a gasar cin kofin duniya.

Neymar mai shekaru 22, ya ji rauni a idon sawunsa a wasansu na zagaye na biyu tsakaninsu da Chile.

Kakakin tawagar Brazil, Rodrigo Paiva ya ce "Likitoci sun duba kafar kuma babu damuwa a kan wasan".

Shi ma kocin Brazil, Luis Felipe Scolari ya ce "Zamu yi kokari don saka shi cikin wasan".

Brazil wacce ke daukar bakuncin gasar cin kofin duniya, za ta buga wasan zagayen gabda na kusada karshe tsakaninta da Colombia.

Karin bayani