Na yi zaton za a fitar da mu - Messi

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lionel Messi na kokarin kafa tarihi da Argentina

Kyaftin din Lionel Messi ya ce ya ji tsoron cewa Switzerland za ta fitar da su daga gasar cin kofin duniya kafin kwallon da Di Maria ya zira a mintin karshe.

Di Maria ya zira kwallon ne bayan da Messi ya tallafa masa abinda ya baiwa Argentina damar kawo karshen turjiyar da Switzerland suka nuna a wasan.

"Gaba na ya fadi lokacin da wasan ya zo karshe saboda mun kasa zira kwallo kuma kuskure kadan ka iya sawa a fitar da mu," a cewar Messi, mai shekaru 27.

"Lokaci na kara tafiya kuma ba ma so wasan ya kai ga bugun fanareti."

Argentina - wadanda suka taba lashe gasar sau biyu sun mamaye wasan amma basu kai ga zira kwallo ba har sai lokacin da Di Maria ya zira kwallon a minti na 118.

A yanzu Argentina za ta kara da Belgium ne a zagayen dab da na kusa da na karshe ranar Asabar.

Karin bayani