Klinsmann ya jinjina wa 'yan wasansa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jurgen Klinsmann

Kocin tawagar Amurka Jurgen Klinsmann ya jinjina wa 'yan wasansa kan irin rawar da suka taka bayan Belgium ta fitar da su a gasar cin kofin duniya.

An fitar da Amurka a gasar bayan da Belgium ta lallasa ta da ci 2-1 bayan an kara lokaci.

Tsohon dan wasan gaban Jamus Klinsmann cewa ya yi, "Ina alfahari da tawaga ta."

Ya kuma kara da cewa, " 'Yan wasan sun taka rawar gani wajen kare martabar kasarsu."

Klinsmann ya ce,"Muna iya kokarinmu wajen za kulo 'yan wasa masu basira a Amurka."