Suarez: Liverpool da Barca za su gana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Luis Suarez ya nemi afuwar Chiellini

Barcelona za ta soma tattaunawa da Liverpool a kan batun sayen dan kwallon Uruguay Luis Suarez.

Ana saran a ranar Laraba mahukunta kungiyoyin biyu za su gana a London don duba yadda za su sasanta game da cefanar da dan kwallon.

Suarez mai shekaru 27, na da sauran shekaru hudu a kwangilarsa tare da Liverpool, kuma kawo yanzu an dakatar da shi tsawon watanni hudu daga murza leda saboda cizon dan kwallon Italiya, Georgio Chiellini a lokacin gasar cin kofin duniya.

Ana tunanin cewar Liverpool za ta amince da tayin fan miliyan 80 a kan Suarez amma kuma wasu bayanai sun nuna cewar Barcelona na sona ta saye shi ne a kan fan miliyan 60.

Watakila a cikin yarjejeniyar Alexis Sanchez ya koma Liverpool.

Luis Suarez ya koma Liverpool ne daga Ajax a shekara ta 2011 kan fan miliyan 22.7.