Ghana 'za ta sauya salo'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kasar Ghana bata taka rawar azo-a-gani ba

Ghana za ta fara shiga kwantaragi da 'yan wasa kafin fara kowace irin gasa don kaucewa sake faruwar badakalar da ta faru a tawagar kasar a gasar cin kofin duniya a Brazil.

'Yan wasan dai sun yi tawaye saboda an ki biyan su kudadensu kafi fara gasar wanda hakan ta sa gwamnatin kasar ta aika tsabar kudi dala miliyan uku don a shawo kansu.

Hukumar kwallon kafa ta kasar ta ce, za ta koma tsarin kulla yarjejeniya tare da biyan 'yan wasa kudadensu ta hanyar Banki.

Haka nan, kocin na Ghana, Kwesi Appiah ya bayyana cewa zai bullo da tsauraran dokoki kan 'yan wasan biyo bayan abin da ya faru a gasar ta bana.

Appiah ya sallami Sulley Muntari da Kevin Prince Boeteng ana tsakiyar gasar saboda nuna halin rashin da'a.

Karin bayani