Afcon 2015: An kori Equatorial Guinea

Equatorial Guinea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mauritania ce ta nuna shakku kan dan wasan

An kori Equatorial Guinea daga wasan kifa daya kwale na shiga gasar cin kofin kasashen Afrika a 2015 saboda sanya dan wasan goge.

Kwamitin shirya gasar ya ce Thierry Fidieu Tazemeta, wanda aka haifa a Kamaru, bai kamata a ce ya buga wasan farko da aka yi a ranar 17 ga watan Mayu ba.

Kwamitin ya ce babu wata shaida da kasar ko Fifa ta bayar da ke nuna cewa dan wasan ya sauya sheka.

Hukumar kwallon kafa ta Caf ta ce hukumar kwallon kafa ta Equatorial Guinea bata bi ka'idojin Fifa ba wurin sanya dan wasan a tawagarta.