Kai tsaye: Faransa da Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan shafi na kawo muku sharhi kai tsaye kan wasan dab da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya tsakanin Faransa da Jamus. Latsa nan domin samun sabbin bayanai.

Mun kawo karshen wannan sharhi da muke kawo muku inda Jamus ta doke Faransa da ci 1-0 domin kaiwa zagayen kusa da na karshe. Da fatan za a ci gaba da kasancewa da bbchausa.com domin samun labarai da dumi-duminsu.

Idan an jima da misalin karfe tara agogon Nigeria da Niger, Brazil za su kara da Colombia. Kuma Jamus na nan tana jiran wanda zai samu nasara.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jamus sun kai wasan kusa da na karshe a karo na goma cikin gasa 13 tun 1966. Kuma sun tsallake zuwa wasan karshe a karo shida daga ciki.
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamus za ta kara a wasan kusa da na karshe da wanda ya yi nasara tsakanin Brazil da Colombia
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An tashi wasa Faransa 0-1 Jamus
Hakkin mallakar hoto BBC World Service

94: Damar karshe ga Faransa - Benzema ya daki kwallon da kafar hagu amma Neuer ya doke kwallon da hannun hagu.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Christoph Kramer (Jamus) ya karbi Toni Kroos

91: Olivier Giroud (Faransa) ya kayar da Schürrle (Jamus).

An kara minti hudu bayan cikar mintina 90.

89: Olivier Giroud (Faransa) ya yi laifi.

87: Jamus sun sake kai kora ta hannun Muller, inda ya mika kwallon ga Schürrle - wanda ya nemi raga amma ta daki dan bayan Faransa, a don haka ta fice ba matsala.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Magoya bayan Jamus na murna a filin wasa na Maracana
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Olivier Giroud (Faransa) ya karbi Valbuena

83: Kwana ga Jamus amma Faransa sun cire kwallon.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mario Götze (Jamus) ya karbi Ozil

81: A daya bangaren kuma Jamus sun ja zari-zuga amma Lloris ya cece Faransa inda ya kade kwallon da Schürrle ya buga da kafa.

80: Faransa sun kai mummunar kora inda aka cushe a ragar Jamus amma sun yi sa'a kwallo ta fita kwana.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Schweinsteiger (Jamus) bayan ya tade Griezmann

78: Bugun tazara ga Jamus bayan da Matuidi ya yi laifi.

76: Faransa sun kai kora ta hannun Matuidi da kafar hagu amma Neuer ya kade kwallon.

74: Jamus sun kai kora ta hannun Muller amma kwallo ta fito babu kowa inda 'yan Faransa suka cire ba tare da matsala ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Faransa na kokarin ganin sun rama kwallon amma har yanzu babu labari
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Remy (Faransa) ya karbi Cabaye
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Laurent Koscielny (Faransa) ya karbi Mamadou Sakho
Hakkin mallakar hoto AFP

68: Muller (Jamus) ya kai kora bayan da Sakho na Faransa ya yi kuskure a baya.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Schürrle (Jamus) ya karbi Klose

63: Faransa sun samu kwana bayan da Lahm ya fitar da kwallo. An bugo amma Benzema ya taba kwallo da hannu, a don haka bugun gida ga Jamus.

61: Valbuena (Faransa) ya kwanta bayan ya yi karo da Schweinsteiger na Jamus.

58: Faransa sun kai kora, Verane ya saka kai amma kwallo ta fada hannun Neuer.

54: Tony Kroos (Jamus) ya kai kora tare da taimakon Bastian Schweinsteiger.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sami Khedira (Jamus) saboda ya yi laifi

53:

48: Bastian Schweinsteiger (Jamus) ya yi laifi.

An dawo zagaye na biyu

Ra'ayi daga shafin BBC Hausa Facebook: Bilya Dogo Dandinshe: Ni ina ganin Jamus za su samu nasara akan Faransa da ci biyu da daya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hummels ne ya zira kwallon a minti na 12
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An tafi hutun rabin lokaci Faransa 0-1 Jamus

An kara minti daya bayan cikar mintina 45 na farko.

43: Karim Benzema ya sake kai kora daga kafar dama ya doka kwallo mai karfi amma Neuer ya cafke kwallon.

42: Faransa sun kai kora ta hannun Benzema amma kwallo ta daki jikin Hummels, sai dai 'yan Faransa na cewa hannunsa ne.

40: Bugun tazara ga Jamus bayan Debuchy ya kayar da dan Jamus.

Sami Khedira (Jamus) ya kwanta bayan da kwallo ta daki fuskarshi.

33: Faransa sun kai kora ta hannun Benzema amma kwallon ta fita kwana bayan da aka cakude a ragar Jamus. An bugu kwanar amma Sakho ya sa kai sai dai ta tashi sama.

30: Kwana ga Jamus - Tony Kroos ya bugu amma Verane ya fitar da ita.

28: Patrice Evra (Faransa) ya kayar da Klose - bugun tazara a gefen hagu kusa da ragar Faransa.

Magoya bayan Faransa sun fara yaushi a cewar Aminu Abdulkadir - yana sharhi kan wasan a BBC Hausa rediyo. Za ku iya saurara a kan mita 16 da kiloHerzt 17685.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tun daga gasar shekara ta 2002 Jamus sun zira kwallaye 15 da ka, bakwai fiye da kowacce kasa a wannan lokaci.

24: Jamus na korafi kan bugun fanareti bayan da Debuchy ya rike Klose.

19: Cabaye ya yi laifi kuma alkalin wasa yi yi masa gargadi.

Ra'ayi daga shafin BBC Hausa Facebook: Kabiru Abdullahi Shanono: Wannan wasan mace ce da ciki ba'a san abinda za ta haifa ba.

15: Wasa ya fara daukar zafi, Faransa sun kai kora amma kwallon bata yi kyau ba domin 'yan Jamus sun fitar da ita.

Hakkin mallakar hoto Getty

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Faransa 0-1 Jamus - Hummels (Jamus) da ka tare da taimakon Kroos daga bugun tazara.

10: Faransa za su yi jifa wanda suka samu bayan sun kai kora.

10: Faransa 0-0 Jamus

7: Karim Benzema ya kai kora da kafar dama amma kwallon ta fita waje. Tare da taimakon Valbuena.

5: Evra ya yi laifi bayan da doke Muller.

3: Jamus na tattaba kwallo suna kitsa abinda suke so su kitsa.

1 an fara wasa Faransa 0-0 Jamus

17:00 'Yna kwallon kasashen biyu da alkalan wasa sun daga tutar wariyar launin fata bayan da kyaftin-kyaftin na ksashen suka yi rantsuwar cewa ba za su nuna wariyar launin fata ba.

16:57: 'Yan wasa sun fito fili kuma an fara taken kasashen biyu inda aka fara da kasar Faransa.

16:57 Idan an jima kuma masu masaukin bake Brazil za su kece raini da Colombia.

16:54 Tsohon dan wasan WalesRobbie Savage - kuma mai yiwa BBC sharhi kan wasanni ya ce yana ganin Faransa za ta doke Jamus da ci 2-1. Kun yarda da shi?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan Faransa Karim Benzema ya zira kwallo uku - Thomas Muller (Jamus ) kwallaye hudu

16:44 Jamus ta fara gasar da kafar dama amma sai dai daga baya wasan ya dan kufce musu, yayin da Faransa ta shiga gasar ba tare da wani fata a kanta ba amma kuma komai na tafiya daidai a gare su.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Filin wasa na Maracana ya dau harami - ga magoya bayan Faransa da kuma na Jamus.

16:36

16:35 Za ku iya bayyana ra'ayoyinku game da yadda wasan ke gudana a shafukanmu na Facebook da kuma Twitter.

16:33 Tawagar Jamus: Neuer, Howedes, Hummels, Khedira, Schweinsteiger, Ozil, Klose, Muller, Lahm (c), Kroos, Boateng.

16:32 Tawagar Faransa: Lloris (c), Debuchy, Evra, Varane, Sakho, Cabaye, Valbuena, Benzema, Griezmann, Matuidi, Pogba.

16:30 Filin wasa na Maracana ya dau harami - Jamus da Faransa na shirin kece raini.