Brazil 2014: Jamus ta fitar da Faransa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mats Hummels ya zira kwallon a minti na 12

Jamus sun kai wasan kusa da na karshe a karo na hudu a jere bayan da suka doke Faransa da ci 1-0.

Dan wasan baya Mats Hummels ne ya zira kwallon da ka a minti na 12 bayan da ya shige gaban Raphael Varane lokacin da Toni Kroos ya yo bugun tazara.

Mai tsaron gidan Jamus Manuel Neuer ya hana Mathieu Valbuena da Benzema zira kwallaye.

Dan Jamus Andre Schurrle ya barar da dama lokacin da ya buga kwallo a kafar golan Faransa Hugo Lloris kafin Neuer ya tare kwallon Karim Benzema a mintin karshe na wasan.

Jamus za su kara da wanda ya samu nasara tsakanin Brazil da Colombia - wadanda za su fafata a daya wasan da za a buga ranar Juma'a.

Karin bayani