Shigar Tim fili ya ba Netherlands nasara

Krul ya tire cin kwallo
Image caption mai tsaron gida Krul a bugun daga kai sai mai tsaron gida

Mai bada horo na Kungiyar kwallon kafa ta Netherlands Louis Van Gaal ya ce tsayin da cika ido da mai tsaron gida Tim Krul ke da shi ne ya sa ya saka shi ya sauya mai tsaron gida na Newcastle a wasan quarter final da suka yi da Costa Rica

Krul wanda yake da tsawon kafa 6 da inchi 4 ya canji Jasper Cillessen mai tsawon kafa 6 da inchi 2 dakikoki kadan a kare wasan da aka tashi babu ci.

Kociyan ya ce shawarar da ya yi na saka dogon mai tsaron gidan ya yi amfani domin kuwa sun sami nasara inda ya kade bugun daga kai sai mai tsaron gida har guda biyu abinda ya basu nasarar gasar.

Netherlands, ita ce Kungiyar kwallon kafa daga cikin wadanda suka fito wasan kusa da na karshe wadda ba ta taba cin gasar kwallon na duniya ba.

Netherlands za ta kara ne da kasar Argentina a filin wasa na Sao Paulo ranar Laraba.

Karin bayani