Kocin Algeria ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Algeria sun taka rawar gani sosai a gasar ta Brazil 2014

Kocin Algeria Vahid Halilhodzic ya yi murabus duk da kiran da shugaban kasar ya yi masa na ya ci gaba da zama.

Dan kasar ta Bosnia ya jagoranci Desert Foxes zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya a karon farko a tarihin kasar inda Jamus ta fitar da su da kyar.

Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika ya nemi Halilhodzic da ya zauna amma ya bayyana "bukatar wani kalubalen" a matsayin dalilinsa na ajiye aikin.

Kocin mai shekaru 61, ana sa ran bayyana shi a matsayin sabon kocin Trabzonspor na kasar Turkiyya.

Karin bayani