Cesare Prandelli ya koma Galatasaray

Cesare Prandelli Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Prandelli ne ya jagoranci Italy a gasar Brazil 2014

Kulob din Galatasaray na kasar Turkiyya ya nada tsohon kocin Italiya Cesare Prandelli a matsayin koci.

Galatasaray sun raba gari da tsohon kocin Manchester City Roberto Mancini a watan Juni.

Prandelli ya yi murabus bayan mummunar rawar da Italy suka taka a gasar cin kofin duniya da ake yi a Brazil.

Kocin mai shekaru 56, wanda ke da ragowar shekaru biyu a kwantiraginsa da Italiya, ya jagoranci kasar zuwa wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Turai a 2012.

Kafin sannan kuwa, ya taka rawar gani a shekarun da ya shafe a Parma da Fiorentina.