Herrera da Shaw na tawagar Man U

Luke Shaw Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luke Shaw ya taka leda a tawagar Ingila a Brazil 2014

Sabbin 'yan wasa biyun da Manchester United Ander Herrera da Luke Shaw za su bi tawagar zuwa Amurka domin atisayi.

Shaw zai kasance da su a birnin Los Angeles a ranar 18 ga watan Juli tare da Wayne Rooney.

Dan Spain Juan Mata da David de Gea suma suna ciki, tare da dan Japan Shinji Kagawa.

"Mun yi murnar samun 'yan wasa masu kwari sosai a wannan atisayin zuwa Amurka," a cewar mataimakin koci Ryan Giggs.

Karin bayani