Yattara zai ci gaba da zama a Lyon

Mohamed Yattara Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mohamed Yattara yana kuma haskaka wa a Guinea

Dan wasan Guinea Mohamed Yattara ya sabunta kwantiraginsa da shekaru biyu a kulob din Lyon na Faransa.

Yattara, mai shekaru 20, ya tafi Lyon ne a 2009 kuma ya shafe mafi yawan shekaru ukun da suka gabata a matsayin aro.

Ya zauna a kulob din Ligue 2 Arles-Avignon, da Troyes na Ligue 1, sannan ya sake komawa Ligue 2 tare da Angers, inda ya zira kwallaye 11.

Dan kwallon ya wakilci kasarsa sau tara inda ya zira kwallaye biyar.