Froome ya janye daga Tour de France

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Da farko an yi fatan Froome zai sake lashe kanbunsa

Mai rike da kanbun gasar tseren keke ta Tour de France Chris Froome ya fice daga gasar bayan da ya yi karo sau biyu a zagaye na biyar.

Dan tseren na Burtaniya ya dawo wasan ne bayan ya fadi sakamakon santsi, sai dai ya janye bayan ya sake faduwa a karo na biyu.

An saka shi a motar kula da marasa lafiya ta Team Sky domin barin gasar.

Froome ya fara wannan zagayen ne a matsayi na bakwai, tazarar dakika biyu a bayan wanda ke jagorantar tseren Vincenzo Nibali.