FIFA ta dakatar da Nigeria

Image caption Maigari ya musanta zargin da hukumomi suka yi masa

Hukumar kula da kwallon kafa ta Fifa, ta dakatar da Nigeria daga harkokin kwallon kafa bayan da kasar ta kori shugabannin hukumar NFF.

Dakatarwar za ta fara aiki nan take - duka tawagar kasar da jami'anta an hana su shiga dukkan wasannin kasashen duniya da kuma na Afrika.

A makon da ya gabata ne aka kori shugabannin hukumar kula da kwallon kafa ta NFF, sannan aka maye gurbinsu da na riko.

Rahotanni sun ce an kama shugaban NFF Aminu Maigari, bayan da ya koma gida daga Brazil bisa zargin aikata ba daidai ba.

Kamun kafa

Fifa, wacce ke adawa da tsoma bakin gwamnati a harkar kwallo, ta baiwa Nigeria zuwa ranar Talata ta mayar da shugabannin hukumar NFF da aka kora.

Hukumar ta kuma sanya ranar 15 ga watan Yuli domin a shawo kan lamarin ko a hana tawagar 'yan kasa da shekaru 20 ta Nigeria shiga gasar cin kofin duniya ta mata.

Nigeria ta ce matakin ya zama wajibi saboda shari'ar da ake yi kan shugabannin hukumar. Sannan ta tura jami'ai zuwa Brazil ciki har da tsohon mamba a kwamitin zartarwa na Fifa Amos Adamu domin kamun kafa.

Gwamnatin ta kuma ce an tura takardun da ke nuna cewa matakin da aka dauka ya yi daidai da dokokin Fifa, a don haka ya kamata a amince da matakin.

Karin bayani