Lloris ya sabunta kwangilarsa a Spurs

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hugo Lloris

Golan Faransa, Hugo Lloris ya sanya hannu don tsawaita kwangilarsa tare da Tottenham don ci gaba murza leda a kungiyar.

Dan wasan mai shekaru 27, wanda ya koma Tottenham daga Lyon a kan fan miliyan takwas a shekara ta 2012, ya buga wa kungiyar wasanni 78 kawo yanzu.

Lloris ne kyaftin din tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya, kuma ya buga duka wasannin kasar guda shiga a Brazil.

Lloris ya ce "Zuwan Mauricio Pochettino na da mahimmanci saboda yana da burin samun nasara."

Golan zai yi aiki a karkashin koci na uku a Spurs, saboda korar Andre Villas Boas da kuma Tim Sherwood.