'FIFA:Gwamnatin Nigeria ta wanke kanta'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An dakatar da AMinu Maigari da mukarrabansa

Ma'aikatar wasanni a Nigeria ta ce babu hannunta a batun tsige shugabannin hukumar kwallon kasar-NFF.

Matakin hukumar wasanni din ya janyo FIFA ta dakatar da kasar daga shiga harkokin kwallon kafa a duniya.

A cewar mahukunta wasanni a Nigeria, sun bi umurnin kotu ne kawai ta hanyar nada kantoma bayan da kotun ta dakatar da shugabannin NFF, karkashin jagorancin, Aminu Maigari.

A yanzu haka dai gwamnatin ta dauki matakin tura wakilai zuwa hedikwatar hukumar ta FIFA don warware wannan matsala.

Idan har ba warware takkadar ma daga nan zuwa 15 ga watan Yuli, to Nigeria ba za ta iya halartar gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 ba, wanda za a soma a wata mai zuwa a kasar Canada.