Brazil 2014: Abubuwar biyar da suka yi fice

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption David Luis ne ya jagoranci Brazil a wasansu da Jamus

Bayan kammala wasannin rukunin farko da suka burge mutane a gasar cin kofin duniya, wakilin BBC na sashen wasanni Stephen Fottrell, ya fitar da wasu muhimman abubuwa da ba za a manta da su ba a gasar ta Brazil 2014.

Yadda aka yi wuju-wuju da Brazil

Duk da irin farin ciki da kuma fitar da tsammani da gasar ta zo da shi, akwai wani abu sama da wadannan, duk da dalilai na rashin gaskiya da daga bangaren mai masaukin baki.

Kimar 'yan wasan Brazil sun kare da zubar hawaye bayan da Jamus ta lallasa ta da ci 7-1 a gaban magoya bayanta da ke fusace cike da dimuwa, yanayin da ba zai gushe ba a idanun wanda ya gani.

Da yawa daga cikin 'yan kasar ta Brazil sun tsoraci tawagar 'yan wasan kasar inda suke kallonta a matsayin mafi farin jini amma kuma marar karfi a gasar cin kofin duniya.

Amma sakamakon goyon bayan da suke samu a duk inda suke buga wasa, hakan zai sa su kai ga zagayen karshe.

Sai dai kash, ba su shirya tinkarar wasan kurar da Jamus ta yi da siu ba a Belo Horizonte wanda ita ce rashin nasara mafi girma da Brazil ta taba fuskanta a harkar kwallon kafa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Klose ya ajiye tarihi

Dan wasan gaban Jamus Miroslav Klose ya zama dan wasa da ya fi cin kwallaye a gasar cin kofin duniya a tarihi inda ya jefa kwallaye 16 bayan ya zira kwallo daya a nasarar da suka samu kan Brazil.

Klose, mai shekaru 36 ya karya tarihin tsohon dan wasan Brazil Ronaldo wanda ke da kwallaye 15.

Dan wasan na Jamus kuma wanda ya fi kowa yawan kallaye a gasar cin kofin duniya, ya ci kwallaye 71 a wasanni 36, shi ne na dan wasa na 3 da ya ci kwallaye a wasanni hudu da ya buga a irin wannan gasa bayan Pele na Brazil da Uwe Seeler.

Raunin Neymar abin tsoro ne

Alamu na rashin tabbas sun bayyan bayan da tauraron Brazil Neymer ya samu rauni a wasan da suka buga da Colombia inda aka yi waje da dan wasan bayan ya samu karaya a gadon bayansa lokacin da Juan Zuniga ya masa gula.

Haka kuma Brazil ta sake rasa wani tauraron Thiago Silva sakamakon dakatar da shi da aka yi.

Rodriguez dan wasan gaba mai rikitarwa

Dan wasan gaban Columbia wanda ke takarar Golden Boot ya zira kwallaye biyu a wasansu da Uruguay inda hakan ya sa ya ajiye tarihi a Gasar.

Ya kuma ci wata kwallo mai ban sha'awa a wasan.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan lamari ya ja hankalin masu sha'awar kwallo

Krul ya tsugunar da Costa Rica

Kafin wasan da suka yi canjaras da ta kai su ga bugun finareti da Argentina, Netherlands sun yi wani wasa mai kama da al'amara tsakaninsu da Costa Rica a wasan dab da kusa da na karshe.

Sai dai kocin Netherlands Louis van Gaal ya yi wata kasassaba inda ya canza mai tsaron gida Tim Krul da Jasper Cillessen a karshen lokacin da aka kara.

Krul duk da bai taba wasa a gasar ba, ya yi nasarar tarbe kwallaye biyu a bugun finariti inda ya kai kasar ga gaci.

Karin bayani