Fifa ta fitar da sunayen zakarun Brazil

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a sanar da zakarun da aka zaba bayan wasan karshe na gasar ranar Lahadi

Fifa ta bayyana sunayen 'yan wasan da za a zabi zakaran 'yan wasan gasar cin kofin duniya da ake shirin kammalawa a Brazil, da zai karbi kyautar Golden Ball.

Argentina tana da 'yan wasa uku da suka kunshi, Angel Di Maria da Javier Mascherano da Lionel Messi.

Abokiyar karawarta a wasan Karshe na gasar ranar Lahadi, Jamus take da 'yan wasa hudu.

'yan wasan su ne, Mats Hummels da Toni Kroos da Phillip Lahm da Thomas Muller.

James Rodriguez na Colombia da Neymar na Brazil da Arjen Robben na Holland su suka kammala sunayen 10.

Fifa ta kuma bayyana sunayen masu tsaron gidan da za a zaba da zai karbi kyautar safar hannu ta zinare, wanda ya fi a cikin gololin.

Golan Costa Rica Keylor Navas da na JamusManuel Neuer da na Argentina Sergio Romero.

A bangaren kyautar matashin dan wasa na gasar kuma, akwai Memphis Depay na Holland da Paul Pogba da Raphael Varane na Faransa.

Karin bayani